Ina nan daram a Bayern Munich — Guradiola

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona ta lallasa Bayern da ci uku da nema a gasar Zakarun turai

Kocin Bayern Munich Pep Guardiola ya ce ba zai bar kungiyar ba a kakar wasa mai zuwa, duk da rahotanni da ke cewa Manchester City na zawarcinsa.

Guardiola ya ce "Na riga na fadi sau miliyoyi, zan kasance a nan a kakar wasa mai zuwa. Shi ke nan."

Ya kara da cewar "Ina da sauran shekara daya a kwangila ta."

Kocin City, Manuel Pellegrini na fuskantar matsin lamba tun bayan da Chelsea ta lashe gasar Premier ta bana.

Jaridu a ranar Lahadi sun ba da rahoto cewa Guardiola ya cimma yarjejeniyar komawa Manchester City.

Guardiola ya lashe gasar lig sau biyar a kakar wasa shida a matsayinsa na manaja.