Arsenal za ta iya lashe kofin Premier badi

Arsene Wenger
Image caption Arsenal tana mataki na uku a teburin Premier bana

Arsenal za ta iya lashe kofin Premier badi idan ta dace da ci gaba da murza leda mai kayatar wa, in ji Arsene Wenger.

Rabon da Arsenal ta dauki kofin Premier tun a shekarar 2003-04, yayin da take fatan karewa a mataki na biyu a gasar Bana.

Wenger ya ce "Ba zaka iya lashe wasanni 38 da salon murza leda guda daya ba, kana bukatar daidaito, idan ma ba ka kan ganiyarka za ka iya cin wasa".

Kociyan ya ce masu tsaron bayansa hudu sun ishe shi tunkarar gasar badi ba tare da ya sayo sabbin 'yan wasan baya ba.

Wenger ya ce zai ci gaba da amfani da Laurent Koscielny da Per Mertesacker da Calum Chambers da kuma Gabriel kuma idan an samu matsala Mathieu Debuchy da Nacho Monreal za su iya dinke baraka.