Barcelona ta kai wasan karshe a kofin zakarun Turai

Neymar
Image caption Barcelona ta dauki kofin zakarun Turai sau hudu a tarihin gasar

Barcelona ta kai wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, duk da doke ta 3-2 da Munich ta yi ranar Talata a Jamus.

'Yan wasan da suka ci wa Bayern Munich kwallaye sun hada da Benatia da Lewandowski da kuma Mullar, yayin da Neymar na Barcelona ya ci kwallaye biyu.

A wasan farko da suka yi a Barcelona 3-0 aka doke Munich a Spaniya, a inda Messi ya ci kwallaye biyu a wasan Neymar kuma ya ci daya.

Barcelona za ta jira wacce za ta kara da ita a wasan karshe a gasar kofin bana tsakanin Real Madrid da Juventus.

Juventus ce ta doke Real Madrid 2-1 a Italiya a wasan karon farko da suka yi a makon jiya.