Hazard ya lashe kyautar marubuta labaran tamaula

Eden Hazard Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Eden Hazard ya haskaka a gasar wasannin bana

Eden Hazard ya lashe kyautar gwarzon dan wasan tamaula na bana da yafi yin fice wanda hukumar marubuta labaran kwallon kafa ta sanar.

Hazard, dan kasar Belgium, ya lashe kyautar ne da kaso 53 cikin 100 daga cikin 'yan jaridu sama da 300 da suka kada kuri'un.

Dan wasan, mai shekaru 24 shi ne ya zama gwarzon dan kwallon gasar Premier na bana da aka karrama a cikin watan Afirilu.

Dan kwallon Tottenham Harry Kane ne ya zamo na biyu a zaben da aka yi, yayin da kyaftin din Chelsea John Terry ya zama na uku a zaben.

Hazard, wanda ya koma Chelsea a shekarar 2012, ya ci wa Chelsea kwallaye 20 a dukkan wasannin da ya yi a kakar bana.