Monk bai damu da korafin Wenger ba

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Arsenal tana mataki na uku a teburin Premier, za kuma ta ziyarci Man United ranar Lahadi

Kociyan Swansea City Garry Monk ya kare zargin da koci Arsene Wenger ya yi masa cewar sun ki taka leda kamar yadda ya kamata.

Wenger ya yi wannan ikirarin ne bayan da Swansea ta doke su da ci daya mai ban haushi a gasar Premier ranar Litinin a Emirates.

Bafetimbi Gomis ne ya ci Arsenal kwallo saura minti biyar a tashi wasan duk da matsin da suka sha a hannun Gunners din.

Wenger ya ce "Munyi rashin nasara ne a hannun kungiyar da ta tare bayanta ta ki amincewa ta fito a murza leda".

Sai dai monk ya maida wa Wenger martani a inda ya ce "Da ba su yi wasa ba da ba su samu maki uku a kan Arsenal ba".

Wannan shi ne karon farko da Arsenal ta yi rashin nasara a wasa bayan da ta lashe fafatawa 11 da ta yi a jere a baya.