Rodriguez ya sabunta kwantiragi a Southampton

Jay Rodriguez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jay Rodriguez ya yi jinyar shekara daya, sakamakon karye wa da ya yi a kafarsa

Jay Rodriguez ya tsawaita kwantiraginsa da Southampton, a inda zai ci gaba da yi mata wasa har zuwa karshen kakar 2019.

Dan wasan mai shekaru 25, rabonsa da murza leda tun a cikin watan Afirilun 2014, bayan da ya karye a kafarsa, amma ya koma yin atisaye a kwanakin nan.

Rodriguez ya koma Southampton daga Burnley ne a shekarar 2012, kuma ya ci wa kulob din kwallaye 21 tun lokacin da ya koma can da taka leda.

Sai a shekarar 2016 kwantiraginsa zai kare da Southampton, bayan da ya amince ya kara tsawaita zamansa, a inda ya ci kwallaye 17 a kakar wasan bara.

Dan kwallon ya kuma fara buga wa tawagar kwallon kafar Ingila a cikin watan Nuwambar shekarar 2013 lokacin da ta yi wasa da Chile.