Juventus ta fitar da Madrid a kofin zakarun Turai

Juventus FC
Image caption Rabon da Juventus ta kai wasan karshe a kofin zakarun Turai tun a shekarar 2003

Juventus ta kai wasan karshe a kofin zakarun Turai, bayan da suka tashi wasa 1-1 da Real Madrid a karawar da suka yi ranar Laraba a Bernabeu.

Madrid ce ta fara cin kwallo a bugun fenariti da Cristiano Ronaldo ya ci, bayan da Giorgio Chiellini ya yi masa keta a cikin da'ira ta 18.

Juventus ta farke kwallonta ta hannun Morata minti na 12 da aka dawo daga hutun rabin lokaci a fafatawar.

A karawar farko da suka yi a Italiya a makon jiya Juventus ce ta doke Madrid da ci 2-1, kuma jumullar haduwa anci Madrid kwallaye 3-2 kenan.

Juventus wacce ta dauki kofin zakarun Turai karo biyu za ta kara da Barcelona wadda ke da kofin karo hudu a wasan karshe a ranar 6 ga watan Yuni a Berlin.