Nijar ta nada sabon kocin tawagar Mena

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Francois Zahoui a lokacin da yake jagorantar Ivory Coast

Jamhuriyar ta nada Francois Zahoui a matsayin sabon kocin tawagar 'yan kwallon kafar kasar da ake kira 'Mena'.

Zahoui wanda tsohon kocin Ivory Coast ne, zai soma jan ragamar kasar a wasan neman cancantar buga gasar cin kofin Afrika tsakanin Nijar da kasar Namibia a ranar 14 ga watan Yuni.

Ya jagoranci tawagar Elephants ta Ivory Coast zuwa wasan karshe na gasar cin kofin Afrika a shekarar 2012, inda kasar Zambia ta doke su.

Zahoui mai shekaru 52, a kwanakin baya ne aka kore shi a kungiyar AS Kaloum ta kasar Guinea.