An ci tarar Aston Villa kudi £200,000

Aston Villa Pitch invasions Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aston Villa za ta kara da Arsenal ranar 30 ga watan Mayu a Wembley

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar Aston Villa kudi £200,000, bisa shiga filin wasa da magoya bayanta suka yi a gasar kofin kalubale da suka buga da West Brom.

Wasu magoya bayan Villa sun shiga filin tun kafin a tashi daga karawar, yayin da aka dunga yin fatali da kujeru a sashin wajen 'yan kallo baki a ranar 7 ga watan Mayu.

Aston Villa ce ta lashe fafatawar da ci 2-0, lamarin da yasa za ta kara da Arsenal a wasan karshe ranar 30 ga watan Mayu.

Haka kuma hukumar kwallon ta gargadi Villa da ta guji kara aikata laifin da ta yi a nan gaba, ko kuma ta fuskanci hukunci mai tsauri.

Bayan da aka tashi daga wasan kocin, West Brom Tony Pulis ya soki masu kula da filin da yin sakaci, har ma ya ce an saka rayuwar 'yan wasansa a cikin hatsari.