Kotu ta ce a karasa sauran wasannin La Liga

Ronaldo Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona na fatan lashe wasa daya ta tauki kofin La Ligar bana

An amince da a karasa sauran wasannin kasar Spaniya, yayin da aka kawo karshen mako guda da hukumar kwallon kafar kasar ta dakatar da ci gaba da wasannin.

Hakan kuma ya kawo karshen yajin aiki da kungiyar 'yan wasan kwallon kafar suka shiga kan takaddama tsakanin gwamnati da hukumar kwallon kafar kasar.

Wata babbar kotu ce ta yanke hukuncin cewar yajin aikin da kungiyar 'yan wasan suka shiga dangane da hakkin nuna wasannin kasar a talabijin ba ya bisa kan ka'ida.

Da kuma wannan hukuncin, za a ci gaba da sauran wasanni biyu da suka rage a gasar cin kofin La Liga da kuma wasan karshe na Copa del Rey.

Tun farko hukumar kwallon kafar kasar da kungiyar 'yan wasa ne ba su amince ba yadda hukumar dake gudanar da gasar La Liga ke raba kudaden hakkin nuna wasannin kungiyoyin a talabijin.

Barcelona za ta kara da Atletico Bilbao a wasan karshe na Copa del Rey ranar 30 ga watan Mayu a Nou Camp.

Ga wasu manyan wasannin da za a yi a Spaniyar.

Lahadi 17 Mayu: Atletico Madrid v Barcelona da kuma Espanyol v Real Madrid

Asabar 23 Mayu: Barcelona v Deportivo da kuma Real Madrid v Getafe

Asabar 30 Mayu: Copa del Rey final - Athletic Bilbao v Barcelona (Nou Camp)