An kori ministan wasanni a Ivory Coast

Image caption 'Yan wasan Ivory Coast a lokacin da suka lashe gasar

An kori ministan wasanni na kasar Ivory Coast, Alain Lobognon, a yayinda ake ci gaba da bincike kan kin biyan 'yan wasa kudin garabasa na lashe gasar cin kofin Afrika a 2015.

Lobognon ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa shugaban kasa ya ce a sallame shi daga mukaminsa.

Gwamnatin Ivory Coast ta yi abun kunya na kin biya 'yan wasan kwallon kasar kudin da ta yi musu alkawari na lashe kofin Afrika da suka yi a Equatorial Guinea a watan Fabarairu.

Bayan shafe lokaci mai tsawo babu labari, kocin tawagar Herve Renard da kuma dan wasa Sereu Die sun nuna bacin ransu.

Die ya ce "Sun yi alkawarin aiko mana da kudin a banki, amma har yanzu shiru ka ke ji."