Barcelona ta dauki kofin La Liga na bana

Barcelona La Liga Champs
Image caption Barcelona ta dauki kofin La Liga na 23 jumulla kenan

Barcelona ta lashe kofin La Ligar Spaniya na bana, bayan da ta doke Atletico Madrid da ci daya mai ban haushi a Vicente Calderon ranar Lahadi.

Barcelona ta dauki kofin bana ne, duk da saura wasa daya da ya rage a kammala gasar, kuma kofi na 23 da ta dauka jumulla.

Messi ne ya ci kwallon a wasan lokacin da suka yi bani in baka tsakaninsa da Pedro kuma kwallo ta 41 da ya ci kenan a gasar La Ligar bana.

Barcelona na fatan lashe kofuna uku a kakar wasan shekarar nan, a yayin da za ta kara da Athletic Bilbao a Copa del Rey ranar 30 ga watan Mayu da kuma kofin zakarun Turai da za ta fafata da Juventus ranar 6 ga watan Yuni.

Barcelona ta ci kwallaye 108 a gasar, kuma za ta yi wasan karshe da Deportivo La Coruna, a inda Messi da Neymar da Suarez suka ci kwallaye 115 tsakaninsu.

Ga jaddawalin wasannin karshe da za a buga a La Liga ranar 28 ga watan Mayu:

Athletic de Bilbao vs Villarreal CFFC Barcelona vs Deportivo La CorunaCelta de Vigo vs RCD EspanyolMalaga CF vs Sevilla FCReal Madrid CF vs Getafe CFRayo Vallecano vs Real SociedadUD Almeria vs Valencia C.FSD Eibar vs Cordoba CFLevante vs Elche CFGranada CF vs Atletico de Madrid