Kano Pillars ta ziyarci Abia

Nigerian League Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption An shiga mako na 9 a gasar cin kofin Premier Nigeria

Abia Warriors za ta karbi bakuncin mai rike da kofin Premier Nigeria Kano Pillars a gasar mako na 9 ranar Lahadi.

Sauran wasannin da za a yi Giwa FC za ta kara ne da FC Taraba, yayin da Dolphins za ta karbi bakuncin Enyimba ta garin Aba, da kuma wasa tsakanin Shooting Stars da Rangers.

Wikki Tourist za ta barje gumi tsakaninta da Lobi Stars a Bauchi, yayin da Nasarawa United za ta fafata da Sunshine Stars.

A jihar Kano kuwa Bayelsa United ce za ta ziyarci El-Kanemi Warriors, sai kuma Gabros da Sharks su kece raini.

Haka kuma hukumar gudanar da gasar cin kofin Premier ta dage fafatawa tsakanin Kwara United da Warri Wolves.

Ga wasannin da za a buga gasar mako na 9:

  • Gabros FC v Sharks
  • Giwa FC v FC Taraba
  • Dolphins v Enyimba
  • El-Kanemi Warriors v Bayelsa United
  • Wikki Tourists v Lobi Stars
  • Heartland v Akwa United
  • Shooting Stars v Rangers
  • Nasarawa United v Sunshine Stars
  • Abia Warriors v Kano Pillars