Zenit St Petersburg ta lashe kofin Rasha

Zenit St Petersburg Fans Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Zenit St Petersburg ta dauki kofi na uku kenan a cikin shekaru biyar da suka wuce

Kungiyar Zenit St Petersburg ta lashe kofin gasar League din Rasha na bana, duk da tashi wasa kunnen doki da ta yi da FC Ufa ranar Lahadi.

Zenit ta dauki kofin bana ne duk da sauran wasanni biyu suka rage a kammala gasar, kuma kofi na uku kenan da ta lashe a cikin shekaru biyar da suka wuce.

Dan wasan Zenith Hulk na Brazil ne ya fara cin kwallo a raga daga bugun tazara, a inda Ufa ta farke kwallo ta hannun Haris Handzic.

Zenith wacce koci Andre Villas-Boas ya ke horar wa tun daga watan Maris din 2014, ta kammala gasar bara a mataki na biyu a lokacin da CSKA ta dauki kofin da tazarar maki daya.

Viallas Boas dan kasar Portugal shi ne koci na uku daga kasar waje da ya lashe kofin gasar Rasha, bayan Luciano Spalletti dan Italiya a shekarun 2010 da 2012 da kuma dan Netherlands Dick Advocaat wanda ya dauka a shekarar 2007.