De Gea ya shiga tsaka mai wuya

David De Gea
Image caption David De Gea dan kwallon Spaniya ya taka rawar gani a Manchester United

Kocin Manchester United, Louis van Gaal ya bayyana alamun cewar za su iya yin rashin golansu David De Gea zuwa Real Madrid.

De Gea ya ji rauni a karawar da suka tashi kunnen doki da Arsenal a ranar Lahadi a gasar Premier, kuma kila ba zai buga wasan karshe da United za ta yi da Hull City ba.

Hakan ne yasa ake hangen dan kwallon ya gama wasansa a Old Trafford kenan, zai koma buga gasar La Ligar Spaniya a badi da Real Madrid.

Real Madrid ta yi shirin daukar De Gea domin ya maye gurbin Iker Casillas, kuma Van Gaal ya ce golan zai iya komawa Spaniya domin gida ne a wajensa kuma zai sadu da iyalai da kuma budurwarsa.

Kocin dan kasar Netherlands ya ce ba shi da tabbaci idan Madrid ta taya mai tsaron ragar, amma De Gea yana tsaka mai wuya kan zabar inda zai buga wa tamaula tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa biyu, amma za mu yi murna idan ya zabi ya ci gaba da zama da mu.

Idan har De Gea ya amince zai bar Old Trafford a bana, United za ta yi amfani da Victor Valdes wanda ya bar Barcelona a Janairu ya rattaba kwantiragin watanni 18 a United.