Uefa za ta cire dokar dai-dai ta kashe kudi

Michel Platini Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A shekarar 2011 ne Uefa ta kafa dokar kayyade kashe kudaden kungiyoyin kwallon kafar Turai

Hukumar kwallon kafar Turai Uefa tana shirin dakatar da dokar kayyade kashe kudin kungiyoyi da ta kirkira a shekarar 2011.

A wata hira da aka yi da shugaban Uefa, Michel Platini a wata kafar yada labarai ya ce dokar ta yi amfani sosai, amma za a daina amfani da ita a karshen kakar bana.

A kakar wasan bara sai da hukumar kwallon kafar Turai ta ci tarar Manchester City da Paris St-Germain kan samunsu da aka yi da karya dokar.

Janar sakatare na Uefa,Gianni Infantino ya shaida wa BBC cewa hukumar tana tattauna wa da manyan kungiyoyin kwallon kafar Turai domin yi wa dokar kwaskwarima.

Uefa ta kirkiro dokar ne domin kungiyoyi su dunga kashe kudade da biyan albashi da sauran dawainiyar kwallon kafa dai-dai da aljihunsu.