West Brom ta doke Chelsea da ci 3-0

Saido Berahino Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne wasa na uku da aka doke Chelsea a gasar Premier bana

West Brom ta samu nasara a kan Chelsea da ci 3-0 a gasar Premier wasan mako na 37 da suka buga ranar Litinin.

Saido Berahino ne ya fara cin kwallo daga tazarar yadi 20, sannan ya ci ta biyu a bugun fenariti bayan da John Terry ya yi masa keta a cikin da'ira ta 18.

West Brom ta ci kwallonta ta uku ne ta hannun Christ Brunt a minti na 14 da dawo wa daga hutun rabin lokaci.

Chelsea wacce tuni ta dauki kofin Premier bana ta kammala karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Cesc Fabregas jan kati bisa ketar da ya yi wa Chris Brunt.

Chelsea za ta buga wasan karshe ranar Lahadi da Sunderland a Stamford Bridge, yayin da West Brom za ta fafata ne da Arsenal a Emirates.