Modise ta yi ritaya daga buga tamaula

Portia Modise
Image caption Modise ta fara yi wa Afirka wasa a shekarar 2000 tana da shekaru 16 da haihuwa

Fitatciyar 'yar kwallon tawagar Afirka ta Kudu Portia Modise ta yi ritaya daga buga tamaula nan take, za kuma ta koma neman ilimin horar da tamaula.

'Yar wasan mai shekaru 31 ta ci wa kasarta kwallo ta 100 a raga a wasan da suka casa Algeria da ci 5-1 a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata da aka yi a Namibia a bara.

Haka kuma ta buga wa tawagar Afirka ta Kudu wasanni 117, kuma ta buga wasan karshe ne a lokacin da Ivory Coast ta doke Banyana Banyana a wasan neman mataki na uku a gasar.

Modise wacce aka haifa a Soweto ta fara buga wa kasarta wasan farko tana da shekaru 16 a shekarar 2000, kuma tun daga lokacin ne ta dunga taka rawar gani da tawagar.

A shekarar 2005 tana daga cikin 'yan wasan da aka zabo domin fitar da 'yar kwallon da ta fi yin fice a shekarar, ciki har da 'yar kwallon Nigeria Perpetua Nkwocha.