'Sterling bai tsinana komai ba a Liverpool'

Raheem Sterling Hakkin mallakar hoto
Image caption A shekarar 2017 kwantiragin Sterling zai kare da Liverpool

Tsohon dan kwallon Liverpool John Barnes ya ce Raheem Sterling bai tsinana komai ba a kulob din, kuma ya kamata ya ci gaba da zama har zuwa kakar badi.

Sterling, mai shekaru 20 ya ki ya amince da tayin da Liverpool ta yi masa na ya tsawaita zamansa a kulob din kan kudi £100,000.

Haka kuma ana kyautata zaton cewar dan kwallon Ingila zai nemi izinin barin Anfield a karshen kakar wasan bana a wajen kocinsa Brendan Rodgers.

Ana ta rade-radin cewar zai koma buga tamaula ne da kulob din Manchester City, sai dai Barnes ya ce ba za su dinga saka shi wasa ba akai-akai.

Kwantiragin Sterling zai kare da Liverpool a shekarar 2017, a inda yake karbar £35,000 a duk mako.

Ranar Juma'a babban jami'in Liverpool, Ian Ayre da koci Brendan Rodgers da kuma Raheem Sterling za su tattauna domin lalubo bakin zare.