Sunderland ta ci gaba da zama a Premier

Sunderland Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ta ci gaba da zama a mataki na uku a kan teburin Premier

Sunderland ta tashi wasa canjaras da Arsenal a kwantan wasan gasar Premier da suka buga ranar Laraba a Emirates.

Kafin wasan Sunderland tana bukatar maki daya domin ta kauce wa fado wa daga buga gasar Premier badi.

Arsenal wacce ta kai hare-hare a ragar Sunderland sau 28 kuma 8 suka nufi raga kai tsaye, sannan ta buga kwana guda biyar na fatan kammala gasar bana a mataki na uku.

Da wannan sakamakon Sunderland ta hada maki 38 ta kuma koma matsayi na 15 a kan teburin Premier bana.

Kuma hakan na nufin za a samu cikon kungiya daya da za ta bar gasar bana tsakanin Hull ko Newcastle, bayan da QPR da Burnley suka fara yin ban kwana da Premier a bana.