Xavi na daf da komawa kulob din Al Sadd

Xavi Hernandez Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Xavi Hernandez zai yi wasa a Al Sadd tsawon shekaru uku

Dan kwallon Barcelona Xavi zai sanar da shirinsa na barin kulob din zuwa Al Sadd ta Qatari da zai rattaba kwantiragin shekaru uku in ji eja dinsa.

Xavi, mai shekaru 35, ya kwashe shekaru 17 a Barcelona a inda ya dauki kofin zakarun Turai uku da La Liga uku da karin kofuna bakwai daban-daban a kulob din.

Zai kuma buga wa Barcelona wasansa na karshe a kulob din a karawar da za su yi da Deportivo La Coruna ranar Asabar a gasar La Liga.

A cewar eja dinsa Ivan Corretja, Xavi din zai zama jakada a gasar cin kofin duniya a shekarar 2022, daga nan kuma ya koma neman ilimin horar da tamaula.

Xavi ya wakilci Spaniya wasanni karo 133, ya kuma bayar da gudunmawa a lokacin da kasar ta dauki kofin duniya a shekarar 2010 da kofin nahiyar Turai a shekarun 2008 da kuma 2012.