U20: Ghana ta fitar da sunayen 'yan wasanta

Sellas Tetteh
Image caption Sellas Tetteh na fatan Ghana za ta sake lashe kofin matasan na duniya a karo na biyu

Kocin tawagar Ghana na matasa 'yan kasa da shekaru 20 Sellas Tetteh ya fitar da sunayen 'yan wasa 21 da za su wakilci kasar a kofin matasa na duniya da za a yi a New Zealand.

An nada Joseph Owusu Bempah, a matsayin kyaftin din tawagar wanda ya taka rawa a gasar neman gurbin zuwa gasar a lokacin da aka yi a Senegal.

Hak kuma shima dan kwallon da yake murza leda a Manchester City Yaw Yeboh yana cikin tawagar da ake sa ran zai iya haskaka wa.

Ghana tana cikin rukuni na biyu da ya kunshi Argentina da Austria da kuma Panama a gasar da za a fara daga tsakanin 30 ga watan Mayu zuwa 20 ga watan Yuni.

Ghana ce kasa tilo daga Afirka da ta dauki kofin matasa 'yna kasa da shekaru 20 na duniya a tarihi.

Ga jerin 'yan wasa 21 da Ghana ta fitar da sunayensu:

Masu tsaron raga: Kwame Baah (Heart of Lions), Siedu Muntawakilu (Hearts of Oak), Lawrence Ati-Zigi (Red Bull Salzburg)

Masu tsaron baya: Kingsley Fobi (Right to Dream), Owusu Bempah (Hearts of Oak), Joseph Aidoo (Inter Allies), Joseph Adjei (Wa All Stars), Emmanuel Ntim (Valenciennes), Patrick Asmah (BA United), Patrick Kpozo (Inter Allies)

'Yan wasan tsakiya: Asiedu Attobrah (New Edubiase), Godfred Donsah (Calgliari), Kofi Yeboah (Wa All Stars), Prosper Kasim (Inter Allies), David Atanga (Red Bull Salzburg), Yaw Yeboah (Man City), Clifford Aboagye (Granada), Osei Barnes (Paios Ferriera)

Masu cin kwallo a raga: Benjamin Tetteh (Tudu Mighty Jets), Emmanuel Boateng (Rio Ave), Samuel Tetteh (WAFA)