Figo ya janye daga neman shugabancin Fifa

Luis Figo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Luis Figo tsohon dan kwallon Portugal shi ma ya janye daga takarar kujerar Fifa

Luis Figo shi ma ya bi sahun Michael van Praag kan janye wa daga takarar neman shugabancin kujerar Fifa.

Tsohon dan kwallon Portugal, mai shekaru 42, ya janye ne daga takarar a rana guda da Van Praag shi ma ya janye, domin su marawa Yerima Ali Bin Al-Hussein na Jordan baya a zaben.

Figo ya ce "Blatter zai iya cigaba da jagorantar hukumar Fifa, amma duk da haka sai an gudanar da zabe tukunna".

Mambobin Fifa su 209 ne daga hukumar wasannin kwallon kafa na duniya ne za su kada kuri'unsu.

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a yi zaben a birnin Zurich.