Van Praag ya janye daga takarar shugabancin Fifa

Michael van Praag Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sepp Blatter yana fatan a sake zabensa karo na biyar kan kujerar Fifa a jere

Dan takarar kujerar shugabancin Fifa, Michael van Praag ya janye daga neman jagorantar hukumar, hakan ya sa saura 'yan takara biyu da za su fafata da Sepp Blatter.

Van Praag, mai shekaru 67, shugaban hukumar kwallon kafar Netherlands, ya ce zai mara wa Yarima Ali Bin Al-Hussein na Jordan baya a lokacin zaben da za a yi ranar 29 ga watan Mayun nan.

Daya dan takarar shi ne, Luis Figo, wanda tsohon dan kwallon Portugal mai shekaru 42 yana nan kan bakansa.

Ana hasashen cewar Blatter, mai shekaru 79 ne zai lashe zaben da za ayi, wanda zai bashi damar ci gaba da jan ragamar Fifa karo na biyar a jere.

Tun a watan Fabrairu ne babban sakatare janar na Fifa Jerome Champagne dan kasar Faransa ya janye daga yin takarar kujerar Fifa.