Paolo Maldini ya kafa kulob a Miami

Paolo Maldini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Maldini da Beckham sun taka leda a AC Milan a shekarar 2007

Tsohon dan kwallon Italiya, Paolo Maldini ya bi sahun David Beckham a inda ya kafa kulob din kwallon kafa a Miami na Amurka.

Kungiyar kwallon kafar da ya kafa a Miami, za ta fafata a gasar Arewacin Amurka, wacce gasa ce kasa da ta babbar gasar cin kofin Amurka da ake kira Major League Soccer.

Maldini, mai shekaru 46, ya yi hadakar kafa kulob din ne, da zai kuma yi gogayya da ta Beckham wanda yake fatan kungiyarsa za ta samu gurbin buga gasar MLS nan gaba.

Beckham ya ci karo da cikas kan bukatar da ya mika na son gina filin wasa mai cin 'yan kallo 25,000, a inda mahukuntan Miami suka ki amincewa.

Daga shekarar 2007 zuwa 2012, David Beckham ya buga tamaula a Amurka da LA Galaxy, kuma a watan Fabrairun bara ne ya sanar da aniyarsa ta son kafa kungiyar kwallon kafa a Amurka.