Tottenham ta bai wa Adebayor hutu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Adebayor ya ce 'yan uwansa sun cuce shi a Togo

An bai wa dan kwallon Tottenham, Emmanuel Adebayor hutu domin ya je ya gana da iyalansa a Togo.

Wannan ne karo na biyu da ake bai wa Adebayor hutu a kakar wasa ta bana, domin ya warware matsalolin da yake fama da su tsakaninsa da 'yan uwansa.

Dan kwallon Togo din mai shekaru 31, ya ce saboda matsalolin da ya fuskanta da 'yan uwansa, ya yi tunanin kashe kansa.

Kenan ba zai buga wasansu na karshe ba tare da Everton da kuma rangadin da Tottenham za ta yi a Kuala Lumpur da kuma Sydney.

Adebayor ya koma Spurs ne a shekara ta 2011 daga Manchester City da farko a matsayin aro kafin ya rattaba hannu a kwangila daga bisani.