Ba na tunanin Sterling zai tafi - Rodgers

Hakkin mallakar hoto z
Image caption Sterling ya haskaka sosai

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce yana saran Raheem Sterling ya ci gaba da taka leda a kungiyar har zuwa karshen kwantaraginsa shekaru biyu masu zuwa.

Liverpool ta soke tattaunawa da Sterling a ranar Juma'a saboda kalaman da eja dinsa ya yi.

An ambato eja din Aidy Ward na cewa dan kwallon Ingilan mai shekaru 20 ba zai sabunta kwangilarsa ba ko da an ba shi "£900,000 a duk mako".

Rodgers ya ce "Raheem na da sauran shekaru biyu a kwangilarsa kuma ina saran ya ci gaba."

Rodgers ya ce Sterling na daga cikin wadanda za su bugawa Liverpool a wasanta na karshe a gasar Premier a ranar Lahadi.