Man United ba za ta dauki Falcao ba

Radamel Falcao
Image caption Kwallaye hudu ya ci wa United daga wasanni 29 da ya yi mata

Manchester United ta yanke cewar ba za ta dauki Radamel Falcao ba, idan wa'adin buga mata wasa aro da yake yi da ita ya cika.

A karshen kakar wasan bana ne yarjejeniyar da suka kulla da Monaco za ta cika kan Falcao, kuma a ranar Litinin ce dan wasan zai gana da koci Louis van Gaal.

Tuni United ta ce ba za ta iya sayen dan wasan, mai shekaru 29, kan kudi £43.2m ba, bayan da kwallaye hudu kacal ya ci a wasanni 29 da ya buga mata.

Kafin ya koma United buga tamaula yana daga cikin fitattun 'yan wasa masu cin kwallo, a inda ya zura kwallaye 104 daga cikin wasannin 139 da ya yi a Porto da Atletico Madrid da Monaco.

Dan kwallon ya gamu da cikas bayan da ya ji rauni a watan Janairu wanda ya hana shi buga gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil.