Ronaldo ya ci wa Madrid kwallaye 61 a bana

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption A kakar wasan bara kwallaye 60 Cristiano ya ci wa Madrid

Cristiano Ronaldo ya ci wa Real Madrid kwallaye 61 a kakar wasan bana, yayin da ya ci uku a lokacin da suka doke Getafe 7-3 a La Liga ranar Asabar.

Ronaldo ya ci kwallaye 48 a gasar La Ligar da aka kammala ta bana, a inda ya dara Lionel Messi na Barcelona da tazarar kwallaye biyar.

Kwallaye ukun da Ronaldo ya ci a ragar Getafe a gida shi ne karo na takwas da ya yi haka a bana, sai dai kuma Madrid din ta kare shekarar nan ba tare da daukar kofi ba.

Hakan ne kuma yasa koci Carlo Ancelotti cikin matsi, duk da cewar saura shekara daya kwantiraginsa ya kare da Madrid.

Real Madrid wacce ta dauki kofin La Liga karo 32, ta kammala gasar bana ne a mataki na biyu da maki 92.