Zan fuskanci kalubale a badi — Mourinho

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mourinho ya ce a Premier badi za a fuskanci kalubale

Kocin Chelsea, Jose Mourinho, ya ce idan har yana son kare kofin Premier da ya dauka a bana, tabbas sai ya tashi tsaye a badi, domin zai fuskanci kalubale da dama.

Chelsea ta lashe kofin Premier bana ne tun lokacin da ya rage wasanni uku a kammala gasar, bayan da ta jagoranci teburi tun daga watan Agustan bara.

Mourinho, wanda ya jagoranci Chelsea ta dauki kofin Premier karo na uku, ya ce abokan hamayya ba za su zauna ba suna kallonsu, saboda haka zai kara zage dantse a badin.

Kocin ya kara da cewar a kakar wasannin badi za a yi gumurzu, kuma daya daga cikin dalilan da suka sa ya komo gasar Premier ke nan.

Ana hasashen Manchester City da Arsenal da Manchester United za su kara dauko sabbin 'yan wasa domin tunkarar kakar wasannin badi.