Toure zai ci gaba da murza leda a Man City

Yaya Toure
Image caption An dade ana rade-radin cewar Toure zai bar buga wasa da Manchester City

Yaya Toure zai ci gaba da buga wa Manchester City tamaula a kakar wasannin badi in ji eja dinsa.

Dimitri Seluk ya fada a baya cewar Toure mai shekaru 32 zai bar Manchester City a karshen kakar wasan bana.

Seluk ya fada a wata kafar yada labarai a lokacin da aka yi hira da shi Toure wanda ake rade-radin zai koma Inter Milan wasa, zai ci gaba da buga wa City kwallo.

Toure ya ci kwallaye 10 daga cikin wasanni 29 da ya buga wa City a bana, yayin da kungiyar ta kare a mataki na biyu a kan teburin Premier.

Dan wasan wanda ya koma City daga kulob din Barcelona a shekarar 2010, saura shekaru biyu kwantiraginsa ya kare a Manchester City.