Blatter zai kara durkusar da tamaula — Platini

Blatter Platini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blatter yana fatan a sake zabarsa a matsayi na biyar a jere

Shugaban hukumar kwallon kafar nahiyar Turai, Michel Platini ya ce idan aka sake zabar Sepp Blatter a matsayin shugaban Fifa, harkar kwallon kafa za ta kara ci baya a duniya.

Ranar Lahadi ce za a gudanar da zaben shugaban hukumar ta Fifa, kuma ana hasashen cewar Blatter ne zai lashe zaben karo na biyar a jere.

Platini ya ce idan har Blatter ya ci gaba da shugabantar Fifa, sahihanci da martabar hukumar zai gushe, sannan za ta rasa karfin fada a ji a harkar tamaula.

Haka kuma Platinin ya ce a lokacin shugabancinsa, Blatter ya yi lahani ga martabar hukumar, yayin da kwamitin amintattun hukumar aka zarge su da cin hanci da rashawa, koda yake sun musunta zargin da aka yi musu.

Platini, mai shekaru 59, ya ce zai marawa Yerima Ali Bin Al Hussein na Jordan baya a lokacin zaben neman kujerar shugabancin Fifa a Zurich.