Di Matteo ya raba gari da Schalke

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Di Matteo ya kafa tarihi a Chelsea

Roberto Di Matteo ya ajiye mukaminsa a matsayin kocin kungiyar Schalke ta Jamus, kasa da watanni takwas da kama aikin.

Tsohon kocin Chelsea din mai shekaru 44, an nadashi a watan Oktobar 2014 lokacin kungiyar na matsayin na 11 a yayinda kuma ta kamalla gasar a matsayin na shida.

Di Matteo wanda ya jagoranci Chelsea ta lashe gasar zakarun Turai a 2012, an maye gurbinsa da Rafael Benitez cikin watanni takwas.

Di Matteo ya yi murabus ne bayan rashin jituwa tsakaninsa da daraktan kungiyar Horst Heldt a kan yadda abubuwa za su kasance a kakar wasa mai zuwa.

"Kungiyar na da manufa na daban. Abin da ya sa kenan na ajiye mukami na," in ji Matteo.