Javier Hernandez ya koma Man United

Javier Hernandez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Javier Hernandez ya so ya ci gaba da buga kwallo a Madrid

Javier Hernandez ya koma Kulob dinsa Manchester United, bayan da yarje-jeniyar bayar da shi aro Real Madrid ta kare.

Dan wasan dan kasar Mexico ya je Real Madrid wasa aro ne a watan Satumbar bara.

Hernandez ya ci kwallaye tara a wasanni 33 da ya buga wa Madrid, wacce ta kare a mataki na biyu a teburin La Ligar Spaniya.

Dan kwallon ya buga wa United wasanni 157, yayin da ya ci kwallaye 59, kuma kwantiraginsa zai kare a United din a shekarar 2016.

Real Madrid ce taki daukar Hernandez duk da sha'awar da dan kwallon ya nuna ta ci gaba da murza leda a Spaniya.