An dakatar da golan Ivory Coast buga wasanni 4

Caf Logo
Image caption Caf ta hukunta 'yan wasan ne domin halin rashin da'a da suka yi

An dakatar da golan Ivory Coast Brou Bernard daga buga wasanni hudu, bayan da aka same shi da laifin watsa wa alakalin wasa kasa a lokacin gasar kwallon rairayi.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka ta ci tarar mai tsaron ragar £3,250, wanda ya aikata laifin a lokacin da Madagaska ta fitar da su daga gasar cin kofin Afirka.

Shi kuwa mai tsaron ragar Nigeria Tejiri Rhiogbere an dakatar da shi buga wasanni tsawon shekara daya sakamakon tofawa alkalin wasa yawu da ya yi.

Gola Rhiogbere zai iya fuskantar karin hukunci mai tsauri, bayan da hukumar Caf ta mika rahoton laifin da ya aikata ga Fifa.