'Yan wasa shida ne za su bar QPR

Ferdinand Barton Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption QPR da Burnley da kuma Hull City ne suka bar Premier bana

Rio Ferdinand da Joey Barton na daga cikin 'yan wasa shida da za su bar kungiyar QPR wacce ta bar gasar Premier bana.

Sauran 'yan wasan da za su bar kungiyar sun hada da Richard Dunne da Shaun Wright-Phillips da Bobby Zamora da mai tsaron raga Brian Murphy.

Kuma dukkan 'yan wasan kwantiraginsu da kulob din ya kare ne a karshen kakar wasan shekarar nan.

Sai dai kuma QPR din za ta sabunta kwantiragin Clint Hill da Alejandro Faurlin, yayin da ta bai wa Karl Henry nan da karshen watan Yuni idan zai ci gaba da zama a kungiyar.

QPR ta bar Premier a bana, bayan ta yi shekara daya kacal a gasar, a inda za ta koma buga wasannin Championship a badi.