Sevilla ta sake lashe kofin Europa

Sevilla Dnipro Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sevilla ce kungiyar farko da ta lashe kofin Europa karo hudu jumulla

Kungiyar Sevilla ta Spaniya ta sake daukar kofin Europa da ta lashe a badi kuma karo na hudu, bayan da ta doke Dnipro da ci 3-2 a Warsaw ranar Laraba.

Dnipro ce ta fara zura kwallo a ragar Sevilla ta hannun Nikola Kalinic, kafin Sevilla ta farke kwallo ta hannun Grzegorz Krychowiak.

Nan da nan Sevilla ta kara ta biyu ta hannun Carlos Bacca kuma Rustan Rota ya farkewa Dnipro kwallo wasa ya koma 2-2.

Sevilla ta kara kwallo ta uku ta hannun Carlos Bacca wanda ya bata damar lashe kofin bana, ta kuma samu gurbin shiga gasar cin kofin Zakarun Turai na badi.

Kuma Sevilla din ta kafa tarihin kungiyar da ta fi daukar kofin, wacce ta dauka sau hudu Jumulla, yayin da ta lashe a shekarar 2006 da 2007 da 2014 da kuma bana