Lashe FA zai kara mana martaba — Wilshere

Jack Wilshere Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shekara ta 10 kenan Arsenal tana kammala gasar Premier a matsayi na uku

Jack Wilshere ya ce Arsenal za ta daga martabarta a kakar wasannin bana da ta yi idan ta kara daukar kofin FA da ta lashe a bara.

Arsenal ta kammala gasar Premier bana a mataki na uku bisa teburi, kuma Wilshere ya ce kakar bana za ta yi armashi idan suka doke Aston Villa a Wembley ranar Asabar.

Dan wasan ya kuma kara da cewar da haka ne za a auna kokarin kungiyar, idan ta yi abin azo a gani ko kuma akasin hakan a bana.

Wilshere ya ce sun yi harin su kammala gasar Premier bana a mataki na biyu, yanzu sun mai da hankali kan lashe kofin kalubale.

Dan wasan ya yi fama da jinya a kakar wasannin bana, tun raunin da ya ji a karawar da suka yi da Manchester United a wasan Premier a watan Nuwamba.