Gerrard zai fara yi wa Galaxy wasa a Yuli

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gerrard ya buga wa Liverpool wasanni na tsawon shekaru 17

Steven Gerrard wanda ke daf da barin Liverpool zai fara yi wa sabuwar kungiyar da zai koma wasa La Galaxy ranar 11 ga watan Yuli.

Dan kwallon zai fara murza leda a kungiyar ta Amurka a wasan farko da za ta yi da Club America ta Mexico a gasar International Champions Cup.

Tuni kociyan LA Galaxy Bruce Arena ya ce ya kagu Gerrard ya fara buga wa kungiyar wasa a karkashin jagorancinsa.

Gerrard wanda yanzu yake yin hutu a Dubai tare da 'yan wasan Liverpool, zai koma taka leda a Amurka nan ba da dadewa ba.

Tsohon dan kwallon Ingila ya rattaba kwantiragin shekaru biyu da LA Galaxy, wanda zai bar Liverpool bayan shekaru 17 da ya buga mata wasanni.