Real Madrid na dab da daukar Benitez

Rafael Benitez
Image caption Benitez ya horar da Madrid kungiya ta biyu daga tsakanin 1993 zuwa 1995

Mataimakin shugaban Real Madrid Eduardo Fernandez de Bla ya bayyana alamun cewar suna daf da nada Rafeal Benitez a matsayin sabon kociyan kungiyar.

Benitez zai ajiye aikinsa da Napoli a ranar Lahadi, bayan wasannin karshen Serie A na bana, domin ya maye gurbin Carlo Ancelotti.

Madrid ta sallami Ancelotti duk da lashe kofin zakarun nahiyoyin duniya da ya yi a bana da kuma daukar kofin zakarun Turai da Copa del Rey da ya lashe a bara.

Haka ma Madrid din ta sallami Jose Mourinho a shekarar 2013, bayan da ya daukar mata kofin La Liga daya da kuma Spanish Cup a shekaru ukun da ya yi yana jan ragama.

Benitez mai shekaru 55, ya jagoranci Liverpool a inda ta lashe kofin zakarun Turai a shekarar 2005, ya kuma dauki Europa League a Chelsea a shekarar 2013, sannan ya dauki Coppa Italia da Napoli a shekarar 2014.

Haka kuma kociyan ya dauki kofunan La Liga biyu dana Uefa a Valencia daga tsakanin shekarar 2001 zuwa 2004.