Rodgers zai gana da shugabannin Liverpool

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Brendan Rodgers ya yi shekaru uku yana horar da Liverppol

Brendan Rodgers zai san makomarsa a Liverpool, idan sun kammala ganawa da daya daga shugaban kungiyar Tom Werner.

Werner dan Amurka ana sa ran zai ziyarci Ingila a ranar Laraba, yayin da aka tsara zai gana da Rodgers ranar Laraba domin bitar wasannin da Liverpool ta yi a bana.

Wasu bayanai da suke fitowa daga bangaren Werner da kuma John W Henry na cewa Brendan Rodgers zai ci gaba da jagorantar Liverpool.

Liverpool ta kammala gasar Premier bana a mataki na shida, sannan ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta Badi ba.

Rodgers mai shekaru 42, ya yi shekaru uku yana horar da Liverpool kuma ya ce idan mahukuntan kungiyar sun yaba da aikinsa zai ci gaba da aikinsa.