Liverpool na daf da daukar James Milner

James Milner Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption City ba ta tsawaita kwantiragin Milner ba bayan da ta cika a karshen kakar wasan bana

Liverpool za ta tattauna da Manchester City kan batun daukar James Milner a makonnan, wanda kwantiraginsa da City ke daf da karewa.

Liverpool ta dauki batun daukar dan kwallon da mahimmanci ne domin ta ci moriyar karshen zamansa a City da zai cika.

Tuni ma kungiyar Anfield din tace tana da tabbacin za ta cimma yarjejeniya da dan wasan Ingilan mai shekaru 29.

Idan suka cimma matsaya a tsakaninsu, Milner wanda ya koma City daga Aston Villa a shekarar 2010, zai koma Liverpool ranar 1 ga watan Yuli.

Milner ya fara taka leda a Leeds United, sannan ya koma Newcastle daga nan ya yi shekara daya a Aston Villa sai kuma ya koma City kan kudi £26m.