Damben gargajiya a Dakwa ta Abuja

Alin Tarara Shagon Bahagon Bala
Image caption Alin Tarara daga Arewa da Shagon Bahagon Bala daga Kudu

Ranar Litinin ce za a yi damben karshe na cin gasa a gidan damben Ali zuma dake Dakwa a Abuja Nigeria.

Za a yi manyan wasa tsakanin Ashiru Horo daga Arewa da Mai Caji daga Kudu a damben manya.

Haka kuma Bala Shagon Kwarkwada da Bahagon Sani mai Caji suna daga cikin 'yan damben Kudu da su ma za su yi wasa.

A bangaren Arewa kuwa Dogon dan Bunza da Sojan Kailu ne za su wakilce ta.

Sarkin Dakwa Dr Alasan Musa ne ya saka gasar domin taya murna ga zababbiyar gwamnatin Nigeria karkashin jagorancin Muhammad Buhari.