Newcastle na zawarcin Patrick Vieira

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Patrick Vieira ya nuna sha'awar jan ragama a gasar Premier

Tsohon dan kwallon Arsenal da Manchester City, Patrick Vieira na daga cikin mutane hudu da aka kebe domin nada mutumin da zai zama sabon kocin Newcastle United.

Steve McClaren, wanda Derby County ta kora a makon da ya gabata, shi ma yana cikin jerin.

A cikin wannan makon za a soma tattaunawa da mutanen hudu.

Viera mai shekaru 38, shi ne kocin tawagar 'yan kasada shekaru 21 a tawagar Manchester City.

Tsohon kocin Lyon wanda ya taka leda a Arsenal, Remi Garde na cikin jerin mutanen da ake tunani bai wa dayansu jagorancin Newcastle.

A yanzu haka dai John Carver ne kocin Newcastle tun bayan tafiyar Alan Pardew.