Amurka ta fara bincikar Sepp Blatter

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, Sepp Blatter ya yi murabus

Kafofin watsa labaran Amurka sunce Jami'an kasar sun fara bincikar tsohon shugaban hukumar kallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter, jim kadan bayan ya yi murabus.

Ana binciken Mista Blatter ne a wani bangare na binciken cin hanci da rashawa da ake yi a hukumar ta FIFA.

A makon da ya gabata ne masu shigar da kara na Amurka suka kaddamar da wani bincike kan miyagun laifuka, inda aka kama jami'an FIFA guda bakwai a kasar Suwizalan, cikin mutane 14 da ake zargi.

Blatter ya ce ya yi ritayar ne saboda ya kasa samun goyan baya kan ya kara jan ragamar FIFA daga yawancin al'umma.