Messi aljanin kwallo ne - Buffon

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lionel Messi ya ci kwallaye 58 a raga a wasannin da ya yi wa Barca a bana

Mai tsaron ragar Juventus, Gianluigi Buffon ya ce Lionel Messi aljanin kwallon kafa ne wanda yake taka leda da mutane.

Barcelona da Juventus za su kara a wasan karshe na cin Kofin Zakarun Turai ranar Asabar, kuma Messi na fatan kafa tarihin cin kwallo a wasannin karshe uku na gasar.

Buffon mai shekaru 37 ya ce yana fatan Messi zai yi wasa a siffar dan Adam idan sun zo karawa a ranar 6 ga watan Yuni.

Messi mai shekaru 27 ya ci wa Barcelona kwallaye 58 a wasannin da ya buga mata a kakar wasan bana.

Taka leda da Messi ke yi da Neymar da Suarez ya sa sun ci wa Barca kwallaye 120 a tsakaninsu, kuma sun taimaka ta dauki kofin La Liga da Copa del Rey.