An yi maraba da murabus din Blatter

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yi murna da Sepp Blatter ya sanar da cewar zai yi ritaya daga Fifa

Kamfanonin da suke daukar nauyin gasar wasannin Fifa sun yi na'am da yin ritayar da Sepp Blatter ya ce zai yi.

Masu daukar nauyin wasannin da suka yi farin cikin murabus din da Blatter zai yi sun hada da Visa da Coca-Cola da kuma McDonald.

Blatter ya yanke shawara zai yi ritaya daga Fifa, bisa zargin cin hanci da rashawa da suka mamaye hukumar, da kuma adawa da ake da sake zabarsa karo na biyar.

Kamfanin Visa da Coca- Cola sun ce suna fatan za a samu gagarumin sauye-sauye kan yadda ake shugabantar hukumar.

Shi kuwa McDonald cewa ya yi yana fatan wannan ita ce hanyar farko ta maido da martabar hukumar domin masu sha'awar kwallon kafa a duniya su amince da ita.

A makon da ya gabata ne Fifa ta shiga takaddama, bayan da aka damke wasu jami'anta da ake zargi da cin hanci da rashawa.