Rafael na sha'awar Raheem Sterling

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Benitez ya horar da karamar kungiyar Madrid a shekarar 1990

Rafael Benitez ya ce yana sha'awar Raheem Sterling dan wasan Liverppol a wajen ganawa da 'yan jaridu domin bayyana shi a matsayin sabon kocin Real Madrid.

Tshohon kocin Liverpool ya kammala shekaru biyu da Napoli a ranar Lahadi, ya kuma rattaba kwantiragin shekaru uku da zai yi a Bernabeu.

Da aka tambaye shi kan batun Sterling dan kwallon Ingila ya ce babu abin da zai boye suna daraja dan wasan, amma ba ya wasa a Madrid saboda haka ba zai ce komai ba kan batun.

Sterling ya ki amincewa da tayin albashin £100,000 da Liverpool ta yi masa a duk mako domin ya tsawaita kwantiraginsa, ana kuma rade-radin zai koma Manchester City da taka leda.