Uefa: Watakila Xavi ya lashe kofi na 4

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona tana fatan lashe kofuna uku a kakar wasan bana

Andres Iniesta ya ce Xavi ya cancanci ya dauki kofin zakarun Turai na hudu, wanda hakan zai martaba barin Barca da zai yi a bana.

Xavi mai shekaru 35 zai yi wa Barcelona wasansa na karshe a kungiyar a karawar da za su yi da Juventus a Gasar kofin zakarun Turai ranar Asabar a Berlin.

Dan wasan wanda ya yi shekarun 17 a Barca ya dauki kofuna 24 ciki har dana La Liga da Copa del Rey da suka lashe a kakar wasannin bana.

Iniesta ya ce Xavi amininsa ne kuma yana mai fatan ya dauki kofin zakarun Turai na hudu a ranar karshe da zai yi ban kwanar murza leda a Barcelona.

Ita ma Juventus tana fatan ta lashe kofuna uku a bana, bayan da ta dauki Serie A da kuma na kalubalen Italiya.

Xavi zai koma Qatar taka leda a kungiyar Al Sadd wacce zai rattaba kwantiragin shekaru uku da ita.