'A shirye muke mu karbi bakuncin kofin duniya'

Image caption Babu damar nahiya daya ta karbi bakuncin kofin duniya karo biyu a jere

Mahukuntan Biritaniya sun ce a shirye suke su karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2022 idan an karbe damar daga Qatar.

Ma'aikatar tsaron Amurka da ta Switzerland ne suka yi zargin an yi cuwa-cuwa wajen bayar da bakuncin gasar kofin duniya a shekarar 2018 da kuma 2022.

Sakataren wasannin Biritaniya John Whittingdale ya ce Ingila tana da dukkan abubun da ake bukata wajen karbar bukuncin gasar, ya kuma ce ba zai yi wu Ingila ta karbi gasar ba tun da Rasha za ta karbi bakuncin wasannin 2018.

A dokar Fifa nahiya daya ba za ta karbi bakuncin kofin duniya a shekaru biyu a jere ba.

An yi ta kiraye-kirayen a janye izinin da aka bai wa Qatar karbar bakuncin kofin duniya tun lokacin da Blatter ya ce zai yi murabus kan cin hanci da rashawa a Fifa.

Sai dai musu shirya karbar bakuncin gasar na Qatar sun karyata cewar sun bayar da cin hanci kafin a ba su karbar bakuncin kofin duniyar.